Taron PDP: Atiku Abubakar ya hada cincirindon jama’a a Garin Adamawa
- Jam’iyyar PDP ta hada wani taron da babu babba babu yaro
- Atiku ne ya kaddamar da shirin sa na takarar Shugaban kasa
Dinbin Jama’a ne daga ko ina su ka fito su ka halarci wani babban gangami da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku ya hada a Garin Yola da ke cikin Jihar Adamawa a Ranar Asabar din jiya.
Atiku Abubakar ya kaddamar da shirin tsayawan sa takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019 inda mutane da dama su ka halarci wannan taro da aka yi a Garin Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Kasar.
KU KARANTA: Tinubu da Shugaban APC sun gana da wasu manyan APC
Manyan jiga-jigan PDP irin su Shugaban Jam’iyyar na kasa watau Prince Uche Secondus su ne kan gaba a wajen taron. Sauran wadanda su ke wurin sun hada da Fitaccen Sanatan nan na PDP watau Ben Murray Bruce.
An yi wannan babban taro ne a filin Ribadu Square da ke cikin babban Birnin na Adamawa watau Yola. Jam’iyyar PDP ta buga kirji da yawan jama’an inda ta nemi goyon bayan al’umma a zaben 2019 domin gyara kasar nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng