Yan bindiga sun kashe ma’aikacin CBN a Gusau

Yan bindiga sun kashe ma’aikacin CBN a Gusau

Yan sandan Zamfara sun tabbatar da kisan wani ma’aikacin babban bankin Najeria (CBN), Kabiru zango da wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba suka yi a garin Gusau.

Kakakin yan sandan rundunar, Muhammad Shehu ya bayyana a wata sanarwa ga manema labarai cewa an harbe shi har lahira a gidansa dake Gusau a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa makasan sun shiga kidan marigayin da misalin karfe 3:30 na dare sannan suka harbe shi ta tagar dakin baccinsa.

Shehu ya bayyana cewa a take aka labarta lamarin gay an sanda ta hanyar kiran waya inda a take suka tura jami’ansu wurin, “amma kafin su isa masu laifin sun tsere.”

Yan bindiga sun kashe ma’aikacin CBN a Gusau

Yan bindiga sun kashe ma’aikacin CBN a Gusau

Ya kara da cewa yan sanda sun kai marigayin asibiti cikin gaggawa inda aka tabbatar da mutuwarsa.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na sanar da kudirina na sake takara da wuri – Buhari

Ya ce makasan basu dauki komai na marigayin ba.

Sun kuma bayar da tabbacin cewa yan sanda za su yi bincike domin gano wadanda suka yi aika aikan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel