Idan Allah ya so sabon Kamfanin jirgin Najeriya ba zai kai labari ba – Oby Ezekwesili
- Gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar dawo da kamfanin jirgin sama
- Wata tsohuwar Ministar kasar ta tsinewa kokarin tun kafin ayi nisa
- Ezekwesili ta nuna cewa ba abin da ake bukata a Najeriya kenan ba
Yayin da mutane da dama su ka yaba da kokarin da da Gwamnatin Tarayya ke yi na dawo da kamfanin jirgin saman Najeriya sai aka ji wata Tsohuwar Minista aKasar tana sukar lamarin a shafin Tuwita.
Tsohuwar Ministar ilmin Najeriya Madam Oby Ezekwesili tayi tir da shirin Gwamnatin kasar ke yi na kafa Kamfanin jirgin Nigerian Airways. Ezekwesili tace da Gwamnatin Buhari tayi wa kan ta karatun ta-natsu ta bar wannan maganar.
KU KARANTA: An yi ca a kan Oby Ezekwesili na yi wa Najeriya fatan banza
Oby Ezekwesili ta fito kuru-kuru ta nuna cewa yunkurin Gwamnatin Najeriyar ba zai kai ko ina ba don haka maganin kar ayi kar a fara. Tsohuwar Ministar a lokacin PDP tace ba za a kai ga ci ba duk Gwamnatin Buhari ta hau kujera na-ki.
Ezewesili wanda ta rike Ministar Ilmi da kuma na Ma’adanai a Najeriya a lokacin mulkin Obasanjo tace Kamfanin jirgin sama ba shi ne abin da ke gaban Najeriya ba a halin yanzu don haka ta ke sa rai kar a cin ma nasara domin cigaban kasar.
A halin yanzu Gwamnatin Buhari ta na daf dawo da kamfanin jirgin saman Najeriya bayan shekaru 15 da aka kashe kamfanin. Ita dai wannan Minista a na ta ra’ayin kuskure ne ta fuskar tattalin arziki ayi kokarin dawo da kamfanin na jirgin sama.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng