Yan kungiyar R-APC na majalisar wakilai sun dage sauya shekarsu zuwa mako mai zuwa

Yan kungiyar R-APC na majalisar wakilai sun dage sauya shekarsu zuwa mako mai zuwa

An dage sauya shekar da mambobin kungiyar sabuwar APC a majalisar wakilai suka yi niyan yi a jiya Alhamis, 19 ga watan Yuli zuwa mako mai zuwa.

Hakan na zuwa ne yayinda masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC suka yi taron gaggawa a ranar Alhamis, domin marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya da kuma neman hanyar jan hankalin yan kungiyar sabuwar APC domin kada su fice daga jam’iyyar.

Bincike sun nuna cewa taron ranar Alhamis wanda shugaban masu rinjaye a majalisa, Mista Femi Gbajabiamila ya jagoranta ya fara daga karfe 3:30pm zuwa 5:28pm.

Yan kungiyar R-APC na majalisar wakilai sun dage sauya shekarsu zuwa mako mai zuwa
Yan kungiyar R-APC na majalisar wakilai sun dage sauya shekarsu zuwa mako mai zuwa

An lura cewa yan majalisa daga jihohin Oyo, Benue da Kwara basu halarci taron masu ruwa da tsakin ba.

KU KARANTA KUMA: Takaitaccen tarihin Tsohon Sufetan ‘Yan Sandan Najeriya da ya rasu

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ma bai halarci taron ba, koda dai ya jagoranci zaman majalisa na ranar Alhamis ne.

Haka zalika, mataimakin kakakin majalisa, Yussuff Lasun, ma bai halarci taron ba, sai dai hakan na da alaka da zaben fid da gwani da za’a yi a APC na zaben gwamnan jihar Osun.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel