Najeriya tazo na biyu a yawan masu kanjamau, bayan daukar na farko a yawan masu talauci a duniya

Najeriya tazo na biyu a yawan masu kanjamau, bayan daukar na farko a yawan masu talauci a duniya

- Kanjamau ita ce HIV, muddin ta kai AIDS akwai matsala

- Najeriya ce ta biyu a duniya yawan masu dauke da cutar

- An sami raguwar masu kamuwa da cutar don kulawa da ta qaru

Najeriya tazo na biyu a yawan masu kanjamau, bayan daukar na farko a yawan masu talauci a duniya
Najeriya tazo na biyu a yawan masu kanjamau, bayan daukar na farko a yawan masu talauci a duniya

Bayan Afirka ta kudu, Najeriya ce kasa ta biyu a duniya a kasashe na duniya na yawan masu dauke da cutar kanjamau, ko sida, watau HIV.

Tun bayan da aka gano mai dauke da cutar na farko a kasar nan, a 1982, shekaru 36 da suka wuce, har yanzu babu alamun cutar na raguwa tsakanin masu ita.

Victor Omosehin, Shugaban kungiyar masu dauke da cutar HIV ta Najeriya wato NEPHWAN, shi ya jagoranci taron juyayin wadanda cutar ta hallaka inda ya bayyana yadda cutar ke ci gaba da yaduwa duk da kamfen na yaki da ita da ake yi.

DUBA WANNAN: Kashi 1/5 na 'yan Najeriya ke fuskantar barazanar ambaliya a bana

Dogaro da tallafi daga ketare ke ta'azzara lamuran, wanda ya ke ganin sai duk kungiyoyi da daidaikun mutane sun shiga kamfen din.

Ya ce, da a ce an mayar da hankali sosai wajen yakar cutar kamar yadda aka aka yaki cutar Ebola, da tuni an cimma gagarumar nasara.

Omoshehin yaci gaba da cewa,abun damuwa shine yadda cutar ke yaduwa a tsakanin 'yan luwadi da basu fitowa fili su nemi magani, don tsoron hukuncin daurin shekaru 14.

Cutar Kanjamau, wadda ke karya garkuwar jikin dan adam, an gano cewa tana yaduwa ne tsakanin mutane baayan da ta sami baro jikin birrai wadanda ake kira blue monkeys.

Akwai masu ma ganin cewa cutar, kera ta aka yi a dakunan sirri na duniya don ragewa bakaken fata yawa, wanda hakan dai babu cikakkiyar hujja ya zuwa yanzu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng