Dan majalisa ya ba da tallafin motocin bas 3 da litattafai 10,000 zuwa ga makarantun Bauchi

Dan majalisa ya ba da tallafin motocin bas 3 da litattafai 10,000 zuwa ga makarantun Bauchi

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Katagum a majalisar wakilai, Ibrahim Mohammed Baba Katagum ya bayar da tallafin motocin bas mai zaman mutane 50, da litattafai 10,000 zuwa ga makaratu a jihar Bauchi.

An mika biyu daga cikin motocin ga jami’ar jihar Bauchi Gadau yayinda aka mika daya ga makarantar koleji na Aminu Saleh Azare.

Litattafan guda 10,000 sun hada da na darusa daban-daban wadda za’a rarrabawa makarantun Firamare da Sakandare a Katagum.

Dan majalisa ya ba da tallafin motocin bas 3 da litattafai 10,000 zuwa ga makarantun Bauchi
Dan majalisa ya ba da tallafin motocin bas 3 da litattafai 10,000 zuwa ga makarantun Bauchi

Gwamnan jihar Mohammed Abdullahi Abubakar ne ya gabatar da motocin da takardun dad an majalisan ya bayar tallafi a wani taro da aka gudanar a Azare, hedkwatan karamar hukumar Katagum.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya bukaci tabbatar da Ingawa a matsayin shugaban FCSC

Shugaban jami’ar Bauchi, Faresa Auwalu ba ne yakarbi motocin jami’ar guda biyu yayinda Aminu Isyaku, shugaban kolejin ya karbi nasu.

Da yake gabatar da motocin, Gwamna Abubakar ya yabama dan majalisan bisa wannan karamci da yayi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng