Kulob din Larabawa zai bada Biliyoyin kudi ya saye Ahmed Musa

Kulob din Larabawa zai bada Biliyoyin kudi ya saye Ahmed Musa

Labari ya fara yawo a gari cewa babban ‘Dan kwallon Super Eagles na Najeriya watau Ahmed Musa na daf da shiga cikin littafin tarihi na kwallon Duniya da zarar ya koma wani Kulob a Kasar Larabawa.

Kulob din Larabawa zai bada Biliyoyin kudi ya saye Ahmed Musa
Wani kulob na shirin sayen ‘Dan wasan Najeriya Ahmed Musa

Wani Kulob mai suna Al Nassr Riyad da ke kasar Saudi Arabia ne ke shirin kashe kudi har tsaba Euro fam Miliyan £40, 000, 000 domin ganin ya mallaki babban ‘Dan wasan gaban na Najeriya wanda ke taka leda a Ingila.

‘Dan wasan Kasar Najeriya da yanzu shi ne ya fi kowa yawan kwallaye a Gasar cin kofin Duniya na World Cup ya kara fito da kan sa ne a Gasar bana inda ya zura kwallaye har 2 lokacin da Najeriya ta hadu da Iceland.

KU KARANTA: Zidane ya bi Cristiano Ronaldo zuwa Kungiyar Juventus

Kungiyar Al Nassr da ke babban Birnin Saudi dai na neman raba ‘Dan kwallon mai ‘dan karen gudu daga Leicester City ta Ingila. Yanzu haka kwallon da ‘Dan wasan gaban ya ci ta shiga talla cikin kwallayen FIFA ta Duniya.

Kungiyar a shirya ta ke da ta kashe Euro Miliyan 40 wanda ya kusa Naira Biliyan 20 wajen sayen ‘Dan wasan. A tarihin Najeriya dai ba a taba samun ‘Dan kwallon da yayi kudi kamar haka ba. Babu tabbacin ko Musa zai bar Ingila.

Gwarzon ‘Dan wasan nan na Kungiyar Super Eagles na Najeriya watau Ahmed Musa yayi suna a Duniya yanzu. Kungiyar CSKA Moscow ce ta fara fito da ‘Dan wasan, daga baya kuma ya koma Leicester City na Ingila bayan ‘yan shekaru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng