Jerin zaben da Jam’iyyar APC mai mulki ta sha kashi bayan 2015
Wannan karo mun kawo maku jerin wasu zabe da Jam’iyyar APC ta sha kashi bayan zaben shugaban kasa da aka yi a 2015. Ko da dai Jam’iyyar APC ke mulkin Najeriya, akwai zabukan da ba ta samu nasarar lashewa ba.
Daga cikin zabukan da aka yi kuma APC ta dauki kashin ta a hannu akwai:
1. Zaben Gwamnan Anambra
Jam’iyyar APC ta sha kashi a zaben Gwamnan Anambra da aka yi a karshen bara. ‘Dan takarar Jam’iyyar Dr. Tony Nwoye bai kai labari ba inda Gwamna Willie Obiano na APGA ya zarce.
KU KARANTA: Manyan PDP sun fice daga Jam'iyyar sun sha alwashin ganin APC tayi nasara a 2019
2. Zaben Sanatan Anambra
Bayan Zaben Gwamnan Anambra kuma, APC ta sha kasa a zaben Sanatan Yankin Jihar da aka sake yi. ‘Dan takarar APGA Victor Umeh ne ya lashe zaben bayan Kotu ta tsige Sanata Uche Ekwunife ta APC.
3. Zaben Sanatan Osun
Haka kuma aka yi a Jihar Osun inda Ademola Adeleke na PDP ya dare kujerar ‘Dan uwan sa bayan rasuwar Marigayi Sanatan na Osun ta Yamma. Mudathir Husseini na APC bai kai labari ba a zaben.
4. Zaben Majalisan Jihar Oyo
Kwanakin baya ne Kakakin Majalisar dokokin Jihar Oyo ya rasu. Ko da aka sake zabe domin maye kujerar ‘Dan Majalisa a Yankin Ibarapa, wani Matashi ne daga Jam’iyyar PDP yayi nasara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng