Kotu ta aikawa shugaban INEC sammaci, tana ma wai barazanar daure shi
- Kotu tana bukatar Mahmood Yakubu ya bayyana gabanta, yayi mata bayanin abinda zai hana a daure shi
- Yakubu yana fuskanta shari'a da chiyaman din PDP na jihar Anambra ya kai karar shi
Mai shari'a Stephen Dalyop Pam na babban kotun tarayya da ke Abuja ta umarci chiyaman din I NEC, Farfesa Mahmood Yakubu, da ya gurfana gabanta tare da bayanin abinda zai sa ba zata daure shi ba sakamakon karya dokar kotu da yayi.
Mai shari'ar yayi watsi da dalilin da zai hana Yakubu bayyana a gaban kotun don yin bayanin dalilin da ba zai yi gidan yari na shekara 2 ba.
Kotun koli ta umarci INEC da ta duba Oguebego a matsayin chiyaman din PDP na jihar Anambra.
Kotun ta kuma umarci hukumar zabe da ta karbi jerin masu takara daga kungiyar Oguebego amma INEC ta ki.
DUBA WANNAN: Sabuwar badaqala a NSITF
Ina zamu iya tunawa, a ranar talata, 10 ga watan yuli, kotun ta ce ya gurfana gabanta ko kuma yaje gidan kaso.
Mai shari'a Pam shi ya bada umarnin ta bakin shugaban masu shari'a na kotun koli a ranar Alhamis, 5 ga watan yuli.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng