Lawal Samaila Yakawada da Uba Sani na neman zama Sanata a Kaduna
- Wasu masu ba El-Rufai shawara za su tsaya takarar kujerar Sanata
- Mr. Uba Sani da Lawal Yakawada na neman takara a Jam’iyyar APC
- Manyan na kusa da Gwamnan su na sa ran doke Sanatan da ke kai
A halin yanzu, siyasar Jihar Kaduna ta dauki wani sabon salo inda ake nema ayi kan-kan-kan tsakanin wasu manyan na kusa da Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai kan kujerar Sanata a Jihar.
Yanzu haka dai Uba Sani wanda yake ba Gwamnan shawara game da harkokin siyasa yana neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya. Yanzu haka Sanata Shehu Sani wanda ba ya ga maciji da Gwamnan Jihar ne ke kan kujerar.
Bayan Uba Sani kuma, akwai Lawal Samaila Yakawada wanda yanzu shi ma yana harin kujerar ta ‘Dan Majalisar Dattawa. Yakadawa ya fito ne daga Yankin Giwa yayin da Uba Sani yake Yanki guda da Sanatan da ke kai Shehu Sani.
KU KARANTA: ‘Yan siyasa 3 da za su iya kawowa El-Rufai cikas a zaben 2019
Lawal Samaila Yakawada tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna ne a lokacin Marigayi Gwamna Patrick Ibrahim Yakowa. Lawal Yakawada yana cikin wadanda ake damawa da su a cikin siyasar Gwamnatin Jihar Kaduna.
Yanzu dai ‘Yan siyasar za su buga ne a Jam’iyyar APC inda ake sa ran za ayi zaben fitar da gwani a watan gobe. Akwai wani ‘Dan siyasa mai suna Lawal Adamu Usman wanda ya bar APC kwanaki kuma ba mamki yayi takarar Sanata a PDP.
Jiya kun ji cewa ‘Dan Majalisa mai wakiltan mazabar Kaduna ta tsakiya Majalisar Dattawa watau Shehu Sani, ya ajiye niyyar sa ta takaran kujeran Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2019 inda yake neman ya koma kujerar sa hankali kwance.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng