An ga fastocin Gwamna Ortom dauke da tambarin Jam’iyyar PDP a Garin Makurdi

An ga fastocin Gwamna Ortom dauke da tambarin Jam’iyyar PDP a Garin Makurdi

- Jama’an Benuwai sun shiga gararin inda Samuel Ortom ya sa kan sa

- An ga wasu fastocin tazarcen Gwamnan Benuwan da Jam’iyyar PDP

- Bisa dukkan alamu Gwamnan ya tattara ya fice daga Jam’iyyar APC

An ga fastocin Gwamna Ortom dauke da tambarin Jam’iyyar PDP a Garin Makurdi

Gwamnan APC yayi nisan kira ya fara shirin neman tazarce a APC

Labari ya zo mana yau cewa an ga fastocin tazarcen Gwamnan Benuwai Samuel Ortom da Jam’iyyar PDP a Garin Makurdi. Da alamu dai Gwamnan yayi sallama da Jam’iyyar APC inda ya furta cewa yanzu ba ya APC kuma ba ya ko ina.

Idan ba ku manta ba an yi kokarin zama da Gwamnan bai yiwu ba inda hakan ya nuna cewa Gwamnan na Benuwai bai jin kira a Jam’iyyar APC. Fastocin Gwamnan tare da Jam’iyyar adawa PDP sun fara yawo yanzu a Gari.

KU KARANTA: An kashe sama da mutum 500 a Benuwai da kewaye

Ana zargin cewa Gwamna Ortom ya samu matsala da Uban gidan sa a harkar siyasa watau Sanata George Akume. Sabanin ne ya jawo Gwamnan ya jefa kafar sa daya ta fice daga Jam’iyyar APC mai mulkin da ya lashe zabe a cikin ta.

An dai hangi hotunan neman tazarcen Gwamnan da Hatimin Jam’iyyar PDP a jikin sa. Yanzu dai hotunan sun cika Garin Makurdi wannan nan ne babban birnin Jihar Benuwai. APC dai tana ta kokarin shawo kan Gwamnan na ta.

Babu mamaki Gwamna Ortom bai jin kiran Jam’iyyar APC bayan da ya ki halatar wani zama da Majalisar ta kira ba. Shugaban Jam’iyyar APC na Yankin Arewa Sanata Lawan Shuaibu ya zauna da Akume amma bai iya ganawa da Ortom ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel