Rashin Imani: Wani Mutumi ya kashe wani Yaro kwanaki biyu da sakin mahaifiyarsa

Rashin Imani: Wani Mutumi ya kashe wani Yaro kwanaki biyu da sakin mahaifiyarsa

A safiyar Talata, 17 ga watan Yuli ne al’ummar garin Potiskum suka tashi cikin alhini da bacin rai sakamakon wani lamari da ya faru a garin, Inda wani Mutumi ya halaka yaron tsohuwar Matarsa ta hanyar caka masa wuka.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Muhammad Kawuwale ne ya bayyana wannan labari a shafinsa na Facebook, inda yace wannan Mutumi ya kashe yaron ne kimanin kwanaki biyu kacal da mutuwar aure tsakaninsa da Mahaifiyar Yaron.

KU KARANTA: Ta leko ta koma: Gwamnan jihar Ebonyi ya karyata batun komawarsa APC

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da Matar ta je gidan tsohon Mijin nata tare da danta don ta kwashe kayanta, amma sai suka tarar da shi a gidan bai fit aba, duk da haka ta yi ta maza ta shifa harhada kayan nata.

A lokacin da Mata ke hada yan komatsanta ne, sai Mijin ya mamayeta, inda ya cafki dan, ba tare da wata wata baya dinga caka masa wuka a ciki, har sai ya tabbata ya mutu.

Ganin gawar yaron kwance jinni sauran Matan dake gidan suka kwarmata ihu suna kururuwa, wanda hakan ya janyo hankulan jama’an unguwar, inda suka afka cikin gidan, suka samu nasarar damke bakin mugun, kana suka mika shi hannun Yansanda.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Uwar yaron ta haifeshi ne a wani aure da ta yi kafin ta auri wannan Mijin da ya saketa, kuma ya kashe mata Da, wanda dududu bai fi shekaru hudu ba zuwa biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: