Shugaba Buhari zai yi magana a gaban babban Kotun Duniya
- Fadar Shugaban kasa tace an gayyaci Buhari yayi magana a Birnin Hague
- Shugaban Najeriya Buhari ne kurum aka zaba cikin shugabannin Duniya
- Muhammadu Buhari yana kasar Holland inda ake wani taron Kasashe yau
Mun samu labari cewa an gayyaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Najeriya yayi jawabi a gaban babban Kotun Duniya. Fadar Shugaban kasar ne ta bayyana wannan a jiya.
Kotun nan ta Duniya da ke Hague a cikin Kasar Holland ta Nahiyar Turai ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya zo yayi mata bayani game da rikicin da ake samu a Duniya na kashe-kashen gilla da sauran yake-yake a Duniya.
KU KARANTA:
Shugaba Buhari kurum dai aka gayyata yayi wannan jawabi a Duniya kamar yadda mai magana da yawun sa Femi Adesina ya bayyana. Najeriya dai za ta fito Duniya inda Shugaban na ta zai mike gaban kowa a Duniya yayi jawabi yau.
Kamar yadda Femi Adesina ya bayyana, Shugaban na Najeriya Buhari zai fadi ra’ayin sa ne game da Kotun da aka kafa domin yaki da masu yi wa dokokin Duniya hawan kawara da kuma wadanda aka samu da laifin kashe jama’a babu sababi.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce karya kurum Fadar Shugaban kasar ta gilla inda ta nemi ya amsa laifuffukan da ake zargin Gwamnatin sa da su na kashe wasu jama'a babu gaira babu dalili a Najeriya. Kungiyar IPOB ma ta shirya zanga-zanga.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng