Wata mata ta gwammace bara maimakon nemawa diyarta lafiya

Wata mata ta gwammace bara maimakon nemawa diyarta lafiya

Wata mata ta kekasa kasa ta hana ayi wa diyar ta mai shekaru biyu a duniya maganin cutar daji da ta kama idonta na hagu, domin ta dinga samun sadaka da ita

Ta hana a yiwa diyarta magani saboda tana so take amfani da ita tana karbar sadaka
Ta hana a yiwa diyarta magani saboda tana so take amfani da ita tana karbar sadaka

Wata mata ta kekasa kasa ta hana ayi wa diyar ta mai shekaru biyu a duniya maganin cutar daji da ta kama idonta na hagu, domin ta dinga samun sadaka da ita.

Wata kungiyar taimakon kai da kai mai suna Global Initiative for Peace, Love and Care (GIPLC) ta karbi yarinyar mai suna Aisha Humaira a ranar 12 ga watan Yuli inda aka kwantar da ita a asibitin koyarwa na jami'ar Abuja don yi mata tiyata.

Kungiyar GIPLC tace uwar yarinyar ta ki kaita asibiti saboda tana amfani da ciwon da yarinyar take dashi domin samun sadaka a wurin mutane.

DUBA WANNAN: Karanta irin abinda Obama yayi da kakarsa lokacin da yaje kauyen su

Kungiyar GIPLC ta bude gidauniyar tallafi na Naira 700,000 don biyan kudin aiki da magungunan da za'ayi wa yarinyar.

A ranar Lahadin nan, mahaifiyar yarinyar ta gudu daga asibitin da diyarta tare da bukatar a biya ta.

"Ma'aikatan jinya sun roketa amma ta ki, "

Shugaban kungiyar ta GIPLC, Nuhu Kwajafa ya rubuta a shafin shi na Facebook a ranar Litinin dinnan.

"Bayan kira maras adadi da aka dinga yiwa mahaifiyar yarinyar, daga baya ta amsa kiran. Ta fadi abinda ya karyar min da zuciya. Mahaifiyar yarinyar tana bukatar a biyata kafin ta bari a yi wa diyar ta magani.

"Irin wannan hali na iyayen mara lafiya ace anki kaishi asibiti, wanda kuma hakkin shi ne, gaskiya ta'addanci ne kuma ya kamata a dauki mataki akan irin wadanda suke aikata hakan. Wannan dai dai yake da hana wanda ya isa zabe, yin zabe ko fitowa takara.

"Irin wadannan abubuwan dole a dakatar dasu, ballantana ga yara, wanda cigaban kasar nan ya rataya a wuyan su.

A cikin kwanaki biyu, kungiyar GIPLC ta samu gudummawar Naira 210,000 don biyan kudin maganin yarinyar.

Amma daga baya kungiyar ta dena karbar taimakon kuma ta bukaci yardar wadanda suka bada gudummawar da ayi ma wani mara lafiyan amfani da kudin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng