Karya ne Miji na bai dake ni ba – In ji matar dan wasan Najeriya
- Masu yada labarin kanzon kurege sai ayi hattara
- Ta bayyana dai cewa labarin nan da aka rika yadawa wai Shehu Abdullahi dan wasan Najeriya ya doki matarsa zulake ne kawai
A yau ne aka tashi da labarin cewa dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Shehu Abdullahi, ya yiwa matarsa dukan tsiya wanda har ya tara mata jini a ido, wannan lamari dai ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, inda mutane da dama su kai ta tofa albarkacin bakinsu.
Sai dai matar dan wasan ta musanta wannan labarai da ya zaga a kafar sada zumunta ta hanyar shafinta na sada zumunta na instagram.
KU KARANTA: Ahmed Musa ya baiwa Sarkin Musulmi wata babbar kyauta (Hotuna)
Sumayya Mustapha, matar dan wasan ta wallafa jawabin ne inda ta ce "Ina so nayi amfani da wannan dama wajen kira ga jama'a game da labarin da ake yadawa cewa mijina ya dokeni, wannan labari ba gaskiya bane, domin ni da mijina muna zaune lafiya cikin so da kaunar juna. tunda muka yi aure da shi bai taba daga muryarsa akaina ba balle har ya daga hannu ya dokeni.
Batun idona da aka gani a haka wannan ya faru ne a wani hadari da nayi, amma batun duka da ake cewa wannan ba gaskiya bane. Ina kaunar mijina kamar yadda yake kaunata, kuma mun dauki wannan lamari da ya faru a matsayin jarrabawa daga ubangiji, saboda ubangiji yace ba zai bar dan Adam ba tare da jarabtarsa ba".
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng