Jam’iyyar APC ta fara harin Taraba da Gombe bayan lashe zaben Ekiti
- APC ta fara hangen yadda za ta yi nasara a Arewa bayan lashe zaben Ekiti
- Jam’iyyar na harin Jihohi 2 na Arewan da su ka rage hannun Jam’iyyar PDP
- ‘Dan takarar APC Dr. Kayode Fayemi ya doke Jam’iyyar PDP a zaben Ekiti
Mun fahimci cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta fara neman ganin yadda za ta samu nasara a Jihohi 2 na Arewa watau Gombe da Taraba da su ke hannun Jam’iyyar adawa na PDP a zabe mai zuwa.
Jam’iyyar APC ta fara wannan dogon hange ne bayan lashe zaben Ekiti da tayi a makon da ya gabata. Jam’iyyar APC ta doke PDP kuma za ta karbe mulki daga hannun Gwamna Ayo Fayose mai rikakkar adawa ga Gwamnatin nan.
KU KARANTA: INEC ta gargadi Fayose ya janye kalaman sa ko ya ji ba dadi
Wani Hadimin Shugaban Kasa mai suna Bashir Ahmad ya tabbatarda wannan inda ya fara wani kira na #ReclaimGombe da #ReclaimTaraba. APC ta fara hangen Jihohin Arewan ne bayan ta mamaye kaf Kasar Yarbawa a yanzu.
Yanzu haka dai Jihar Legas, Osun, Ogun, Ondo har da Ekiti sun samu shiga hannun Jam’iyyar APC. Sai dai wani babba a Jam’iyyar watau Festus Keyamo ya nemi APC ta cigaba da kokari kar tayi irin abin da PDP tayi a zaben 2015.
A zaben 2014, PDP ce tayi nasara a Ekiti, sai dai kuma ta fadi zaben Shugaban kasa. Yanzu dai a zabukan Gwamnoni da aka yi bayan 2015, PDP ta iya lashe Bayelsa ne kurum inda ta sha kasa a Kogi, Ondo, Edo da kuma Ekiti a yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng