Batan dabo: Sojoji 23 da motocinsu 8 ne suka bace bayan wani mummunan harin kwantan bauna da ‘yan Boko Harama suka yi wa sojojin
- Artabu tsakanin Sojoji da 'yan Boko Haram ya sanya bacewar wasu jami'an Sojojin tare da motocinsu
- Sai dai har ya zuwa yanzu babu cikakken bayanin ko suna ina
- Jaruman Sojojin dai sun tafi murkushe 'yan Boko Haram din amma aka yi musu kwantan bauna a hanya kafin su karasa
Al'amarin ya faru ne da safiyar ranar asabar wanda a yanzu haka manyan jami'ai guda biyar, da sojoji 18 suka bace, sai kuma manyan motoci guda 8 da suma ba a san inda suka shiga ba.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa ‘yan tada kayar bayan suna daga cikin wadanda ake zaton sun samu nasarar tserewa jami'an sojin a wani sumame da suka kai musu a baya cikin dajin sambisa da kuma tsibirin Chadi.
Wata majiya daga rudunar sojin ta bayyanawa NAN cewa sun kawo farmakin ne tare da afka musu wanda a dalilin hakan da yawansu suka bace ba tare da an san inda suka shiga ba.
Ya kara da cewa motoci uku ne cikin goma sha daya da aka tura cikin dajin kawai suka kai ga dawowa sansanin sojojin dake Maiduguri cikin yanayin rashin nasara.
"A lokacin da sojojin suka samu labarin cewa yan tada kayar bayan sun taru a kan titin Konduga zuwa daidai kauyen Boboshe, nan take suka tafi domin gamawa da su.
"Amma sai dai kash 'yan ta'addan sun afka musu akan hanyarsu ta zuwa wurin, wanda yanzu motoci uku ne cikin goma sha daya da suka tafi suka samu nasarar dawowa, amma ba za a iya bayyana hakikanin abinda ya faru zuwa yanzu ba".
Mazauna yankin Jilli dake karamar hukumar Gubio a jihar Borno, sun tsere daga gidajen nasu sakamakon wasu hare-hare da ‘yan Boko Haram din suka kawo a ranar Asabar din.
KU KARANTA: Ayya: wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers
Rahotanni sun bayyana cewa mayakam na Boko Haram sun sami damar shigowa cikin yankin ne wanda ya kai ga sun farwa mutane hakan yasa jama'a da dama tserewa daga mazaunin nasu.
Wani mazaunin yankin mai suna Malam Bukar Mustapha ya shaidawa NAN cewa sun tsere ne domin ceton rayuwarsu tunda suka samu labarin ‘yan tada kayar bayan zasu sake dawowa kauyen.
"Ranar asabar da yamma ne, muka samu labarin ‘yan Boko Haram zasu sake dawowa domin kawo hari"
"Ina daya daga cikin mutanen da suka gudu zuwa garin Maiduguri, wanda tafiyar ta kai kilomita 45 daga cikin kauyen nan".
Mustapha ya kara da cewa "Ranar lahadi da safe na kira Gubio domin sanin halin da suke, sai aka shaida min ‘yan tada kayar bayan suka kawo hari a garin. Sai dai ya zuwa yanzu ba zan iya bayyana halin da suke ciki saboda bani da cikakken bayani akan hakan".
Sai dai wani mazaunin yankin ya bayyana cewa an sake tura rundunar sojoji zuwa yankin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng