Zaben Ekiti: Gwamna Fayose ya gaza kai bantensa a karamar hukumarsa
- Abubuwa na shirin birkicewa gwamnan jihar Ekiti
- Sakamakon faduwa karamar hukumarsa a zaben gwamnan jihar da aka gudanar jiya
- Yanzu haka dai alkalumma sun nuna yadda dan takarar APC ke gaba a yawan kuri'u
'Dan takarar gwamna na jamiyyar APC a zaben gwamnan da aka gudanar na jihar Ekiti jiya ya yi nasara a karamar hukumar Irepodun/Ifelodun.
Kayode Fayemi wanda ya samu kuri'u 13,869 a karamar hukumar da ta zamo ita ce mahaifar da gwamna mai barin gado Ayodele Fayose, yayin da kuma jamiyyar PDP ta samu kuri'u 11,456.
Duk da cewa akwatin da gwamna Fayose ya kada kuri'a jamiyyar PDP ce ta yi nasara, amma hakan bai sa ta yi nasarar lashe dukkanin karamar hukumar ba.
KU KARANTA: Dawo-dawo: Fayemi ya kama hanyar zama sabon Gwamnan Jihar Ekiti
Tun da farko dai karamar hukumar tana da mazabu 11, inda aka tattara sakamakon na mazabu 11 duka, jimlar adadin wadanda su ka yi rijistar zabe sun kai 66,162, an samu nasarar tantance mutum 27,306, inda kuma mutane kimanin 27,211 suka jefa kuri'arsu, ragowar kuri'u 1362 suka lalace.
Sakamakon zaben dai ya samu sa hannun wakilan jamiyyun APC da PDP da misalin karfe 11 na dare.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng