Shugaban kasar Pakistan zai shiga kurkuku bayan mulkar kasar shekaru, kuma har sau biyu

Shugaban kasar Pakistan zai shiga kurkuku bayan mulkar kasar shekaru, kuma har sau biyu

- A baya ya tsere Dubai bayan da sojojin Musharraf suka yi masa juyin mulki

- A yanzu duk da yana Ingila, yace zai koma gida ya fuskanci hukunci

- Kotu ta yanke masa shekaru 10 a fursun

Shugaban kasar Pakistan zai shiga kurkuku bayan mulkar kasar shekaru, kuma har sau biyu
Shugaban kasar Pakistan zai shiga kurkuku bayan mulkar kasar shekaru, kuma har sau biyu

Kafin kotu ta bayar da dama a tsige shi, shugaban Pakistan, mai kudin gaske, mai fada aji, ya mulki kasar a shekarun 1990s inda Pervez Musharraf ya hambaras dashi, tare da sanya masa takunkumai.

Shugaban kasar Pakistan zai shiga kurkuku bayan mulkar kasar shekaru, kuma har sau biyu
Shugaban kasar Pakistan zai shiga kurkuku bayan mulkar kasar shekaru, kuma har sau biyu

Bayan kashe Benazir Bhutto a 2007, ya sake dawowa kasar inda aka sake zabarsa bayan da aka takura wa Musharraf dole ya sauka daga mulki ya gudu gudun hijira.

Yanzu shima kotu ta same shi da laifuka da suka hada da almundahana da rashawa da karfa-karfa da azurta na gida, laifi da aka yanke masa shekaru 10 kansu a gidan maza.

DUBA WANNAN: Ana can ana sulhu da Kwankwaso

Sai dai kamar da, yaki yarda ya zauna a kasar, amma wannan karon yace zai je ya fuskanci hukunci, duk da matarsa na ingila na jiyyar cutar kansa.

Shi da diyarsa dai za'a kama muddin suka taka kasar ta Pakistan, kuma kamar dai da gaske zasu iya aikata wannan katobara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng