Ofishin FIRS kadai ya tara wa Buhari Tiriliyan biyu da rabi a watannin nan shida na 2018

Ofishin FIRS kadai ya tara wa Buhari Tiriliyan biyu da rabi a watannin nan shida na 2018

- Hukumar FIRS tace ta samu sama da Naira tiriliyan 2.5 na haraji daga watan Janairu zuwa yuni na 2018

- Wannan yana cikin rahoton kudin shiga na rabin shekara da hukumar ta kai wa ma'aikatar kudi

- An bawa kafofin watsa labarai rahoton a ranar juma'a ta hannun Daraktan ma'aikatar watsa labarai, Hassan Dodo

Ofishin FIRS kadai ya tara wa Buhari Tiriliyan biyu da rabi a watannin nan shida na 2018
Ofishin FIRS kadai ya tara wa Buhari Tiriliyan biyu da rabi a watannin nan shida na 2018

Hukumar FIRS tace ta samu sama da Naira tiriliyan 2.5 na haraji daga watan Janairu zuwa yuni na 2018.

Wannan yana cikin rahoton kudin shiga na rabin shekara da hukumar ta kai wa ma'aikatar kudi.

An bawa kafofin watsa labarai rahoton a ranar juma'a ta hannun Daraktan ma'aikatar watsa labarai, Hassan Dodo.

Lissafin kudin ya nuna cewa hukumar ta riga da ta samu kashi 75 cikin dari na kudin d take da burin samu na shekarar.

Rahoton ya nuna cewa an samu cigaba akan kudin da aka samu na shekarar 2017, wanda kashi 42 ne a cikin dari.

Bayani akan kudin ya nuna cewa Naira tiriliyan 1.16 an samo shi ne daga harajin ribar fetur, amma Naira biliyan 636.1 ne aka samu a shekarar 2017.

DUBA WANNAN: Wanda yafi kowa farce a duniya

Daga harajin kudin shiga kamfanin, hukumar ta samu Naira biliyan 680.09,amma Naira biliyan 551.94 aka samu a 2017.

A value Added Tax kuma an samu Naira biliyan 536.52,wanda a shekarar 2017 an samu Naira biliyan 68.84.

Bayan haka, hukumar ta samu Naira biliyan 77.19 a matsayin harajin ilimi, amma Naira biliyan 58.86 ta samu a 2017.

Kudin shiga na Stamp Duties an samu Naira biliyan 7.49,wanda yafi na 2017 da Naira biliyan 2.34.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel