Zaben Ekiti: Matsaloli uku da kan iya kayar da PDP wan-war a zaben gobe

Zaben Ekiti: Matsaloli uku da kan iya kayar da PDP wan-war a zaben gobe

A yayin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana kammala shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti, masu nazarin siyasa sun yi tambihi a kan wasu matsaloli da kan iya saka jama'ar ta Ekiti yiwa PDP juyawa PDP baya.

Jam'iyyar PDP ce a halin yanzu ke mulkin jihar ta Ekiti karkashin jagorancin Ayodele Fayose.

Saidai jam'iyyar PDP na fuskantar barazanar rasa jihar Ekiti daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. Ga wasu daga cikin matsalolin da kan iya kai PDP kasa wan-war a zaben na gobe.

Zaben Ekiti: Matsaloli uku da kan iya kayar da PDP wan-war a zaben gobe

Zaben Ekiti: Matsaloli uku da kan iya kayar da PDP wan-war a zaben gobe

1. Matsalar albashin ma'aikata: Ba boyayen abu bane cewar ma'aikatan jihar Ekiti na bin gwamnatin Fayose bashin albashi na watanni da dama. Wannan dalilin ya saka masu nazarin siyasa ganin cewar ma'aikatan zasu fito domin nuna fushinsu ta hanyar kin dangwala kuriunsu ga PDP.

2. Halin Fayose: Shakka babu, Fayose na daga cikin shugabanni a Najeriya dake da azarbabi da katobara. Wannnan halayya ta Fayose na bawa jama'ar jihar Ekiti haushi.

Jihar Ekiti na daga cikin jihohin Najeriya dake da yawan masu ilimin boko da ko kadan basa jin dadin irin halayyar Fayose dake zubar da mutunci da kimar jihar.

3. Dan takarar PDP: Masu nazarin siyasa sun bayyana cewar, dan takarar jam'iyyar PDP, Farfesa Eleka, Wanda mataimaki ne ga Fayose, bashi da kwarjini a wurin mutanen jihar Ekiti. Kazalika sunansa bai yi amo a tsakanin 'yan siyasar yankin kudu maso yammacin Najeriya na 'yan kabilar Yoruba ba.

Da yawan masu bibiyar al'amuran siyasa dake wajen jihar Ekiti basu jin sunan dan takarar PDP saidai na APC, Kayode Fayemi

da kuma gwamnan jihar mai barin gado, Fayose. Ana ganin cewar nasarar dan takarar PDP, Farfesa Eleka, tamkar nasara ce ga Fayose kuma zai zama rakumi da akala a hannun Fayose.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel