2019: Buhari ya nada Dauda Rarara a matsayin daraktan wakoki na kasa

2019: Buhari ya nada Dauda Rarara a matsayin daraktan wakoki na kasa

Fadar shugaban kasa, ta ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya ta nada shahararren mawakin nan na Kano, Dauda Rarara a matsayin daraktan waka na kasa kan kwamitin magoya bayan Buhari a 2019.

Babban mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin lamuran siyasa, Gideon Sammani, wanda ya bayyana akan a wata sanarwa yace kwamitin zai samu jagorancin tsohon shugaban PDP na kasa, Ali Modu Sharif a matsayin darakta janar.

2019: Buhari ya nada Dauda Rarara a matsayin daraktan waskoki na kasa
2019: Buhari ya nada Dauda Rarara a matsayin daraktan waskoki na kasa

Sauran wadanda aka nada a kwamitin sun hada dad an wasan Nollywood kuma dan majalisar jihar Lagas Hon Desmond Elliot a matsayin babban sakataren labaran kwamitin na kasa, da kuma shugaban ma’aikata na gwamnan jihar Imo kuma dan takarar gwamna a APC, Uche Ugwumba Nwosu a matsayin babban sakatare.

KU KARANTA KUMA: Dambazau ya kaddamar da yaki da yan bindiga bayan harin da aka kai kauyukan Sokoto

An tattaro cewa kungiyar ya sha banban da na kungiyar yakin neman zabe wanda aka nada Rotimi Ameachi a matsayin darakta janar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng