Gwamnatin tarayya ta zuba N2.5bn daga kudin Abacha a motocin daukar kaya 2 domin tallafawa Fayemi – Dan takarar gwamna a PDP

Gwamnatin tarayya ta zuba N2.5bn daga kudin Abacha a motocin daukar kaya 2 domin tallafawa Fayemi – Dan takarar gwamna a PDP

Kolapo Olushola, mataimakin gwamnan jihar Ekiti kuma dan takarar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna da za’a yi a ranar Asabar, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tura biliyoyin naira a motocin daukar kaya domin ayi amfani da su wajen daukar nauyin zaben Kayode Fayemi.

Yayinda yake jawabi ga wasu manema labarai a Ado-Ekiti a ranar Alhamis, Lere Olayinka, daraktan labarai kuma kakakin kungiyar yakin neman zaben Kolapo Olusola (KOCO), yace kudin na daga cikin dala miliyan 321 da aka dawo da su na kudin satan Abacha.

Ya yi ikirarin cewa an dauki dala miliyan 50 na kudin a jirgi daga Abuja zuwa Akure sannan daga bisani aka kai garin Fayemi a Ekiti cikin motocin daukar kaya guda biyu da taimakon dan takarar gwamna na All Progressives Congress (APC).

Sai dai, Wole Olujobi, kakakin kungiyar yakin neman zaben Kayode Fayemi ya karyata zargin.

Gwamnatin tarayya ta zuba N2.5bn daga kudin Abacha a motocin daukar kaya 2 domin tallafawa Fayemi – Dan takarar gwamna a PDP
Gwamnatin tarayya ta zuba N2.5bn daga kudin Abacha a motocin daukar kaya 2 domin tallafawa Fayemi – Dan takarar gwamna a PDP

A halin da ake ciki, wani Jirgin sama mai saukar ungulu ya sauka a sabon gidan gwamnati, Ayoba Villa, Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya ki sa hannu a wasu dokoki hudu da majalisa ta gabatar masa

Jirgin ya sauka ne a gidan gwamnatin jihar da ranan nan. Ana zargin cewa jirgin mai saukar ungulu ya kawo kudade ne gana wani gwamnan Kudu maso kudu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng