Babbar magana: Buba Galadima ya nemi Kotu ta nada shi sabon Shugaban Jam'iyyar APC
- Buba Galadima ya nemi Kotu ta sauke su Oshimhole daga mukaman su
- Shugaban ‘Yan R-APC ya fadawa Kotu cewa APC ba tayi wani zabe ba
- Don haka ne rikakken ‘Dan siyasar ya nemi a damka sa Jam’iyyar APC
Mun ji labari cewa Shugaban rAPC wanda su ka bangare daga uwar Jam’iyyar APC watau Injiniya Buba Galadima ya nemi Kotu ta nada shi a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki.
Kwanan nan ne Shugaban ‘Yan taware na APC (‘Yan R-APC) watau Buba Galadima ya nufi Kotu inda yake roko a soke zaben da aka yi a watan jiya inda aka zabi Tsohon Gwamna Adams Oshiomhole a matsayin Shugaban APC na kasa.
KU KARANTA: Wasu manyan Gwamnonin APC sun yi kus-kus da Tambuwal
Buba Galadima ya nemi a sauke wadanda aka daura kan kujerun shugabancin Jam’iyyar ne saboda a cewar sa ba ayi wani zaben kwarai ba. Injiniya Galadima yace matakin da APC ta dauka a Ranar 23 ga Watan Yuni ta sa su ka kafa R-APC.
Buba Galadima wanda yanzu ana karar sa a Kotu ya bayyana cewa masu yawo a matsayin shugabannin APC ba su da wata madagora a shari’a don babu zaben da aka yi. Don haka ne Shugaban ‘Yan tawaren ya nemi a tsige Kwamred Oshiomhole.
Kafin nan dai Galadima ya nemi INEC ta daina la'akari da Adams Oshiomhole. Tsohon Sakataren Jam’iyyar nan ta adawa ta CPC sun samu matsala yanzu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya sha alwashin tika sa da kasa a zaben 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng