Wasu matan Najeriya sun gigice da son auren Dangote
Tabbass a wannan zamani da muke ciki mafi akasarin yan mata basu da wani buri da wuce mallakar namiji mai tarin dukiya ta yadda za su fantama son ransu.
Hakan c eta kasance a lokacin da labarin bidar matan aure da mai kudin Afrika ya isowa jama’a, inda mata da dama a Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu akan lamarin.
Jaridar Financial Times (FT) ta wallafa cewa attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote na neman matar da zai aura.
Wannan ya sa wadansu mata musamman a kafafen sada zumunta suka rika bayyana bukatarsu ta neman auren attajirin, wanda yanzu ba shi da mata.
Sai dai wasu daga cikin masu sharhi kan lamarin sun ce ba a fahimci ainihin zancen attajirin ba, don a cikin kalaman da ya yi wa jaridar ta FT, bai fito kai tsaye ya ce yana neman matar da zai aura ba.
Ko ita ma jaridar ba ta sanya wannan magana a matsayin kanun labarin nata ba, sai dai wasu jaridun da suka dauki labarin ne suka sanya hakan a matsayin kanunsu.
"Shekaruna suna kara ja. Shekara sittin ba wasa ba ne...babu amfani na fita neman (aure) kuma idan ka samu ba ka da lokaci," in ji Dangote kamar yadda ya bayyanawa jaridar.
Aisha Falke mai shafin Instagram na northern_hibiscuss ta wallafa labarin Dangoten kuma shaida mana cewa ta samu dimbin sakonni daga mata wadanda suke namen attajirin ya aure su.
Aisha ta kara da cewa: "Tun a ranar da na sanya labarin a shafina, mata suke ta turo min sakonni har da kiran waya, cewa na yi musu hanya.
"Sun yi tsammanin ko ta wajena ya zo neman auren, ba su san cewa ba ni da ko wacce irin alaka ko kusanci da Dangote ba, labari kawai na gani na sanya musu."
Ga ra'ayoyin wadansu mutane da muka samu da shafin Instagram a Najeriya:
zakiyamusajibril "Tirkashi ai har sai ya rasa wadda zai zaba don zai samu issasun masoya."
khaxeenerh_yaree "Tou ta ina ake samo shi bai ba da inda za'a same shi ba."
jrabdulmalik "zan iya nema wa kanwata(aurensa) don ba ta kan Intanet yanzu...tana da gogewa kan zaman aure na tsawon shekara hudu, na bukace ta da ta kashe aurenta tun bayan da na ji labarin nan."
KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi Allah wadai da harin jihar Sokoto, ya sha alwashin kare yan Najeriya
Sai dai kuma akwai wadanda suka yi wa attajirin addu'a da kuma ba shi shawara, kamar haka:
hafcerthassan: "Allah ya ba shi ta gari wacce za ta so shi tsakani da Allah."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng