Buhari ya yi Allah wadai da harin jihar Sokoto, ya sha alwashin kare yan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen mutane da dama da aka yi a ranar 9 ga wataYuli, cikin wadanda aka kashe harda hakimin wani yanki, a kewayen kauyen Gandi a karamar hukumar jihar Sokoto.
Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasa a wata sanarwa a Abuja a ranar Laraba ya kawo cewa gwamnatin Buhari na aiki tukuru domin bayyana masu daukar nauyin wannan mumunan aiki.
Shugaban kasar ya ba yan Najeriya tabbacin cewa za’a zakulo wadanda ke hallaka bayin Allah a kasar sannan kuma sai an yi nasara a kansu.
Ya yi alkawarin cewa duk day an ta’addan na amfani da dabarun da ba’a gane ba tukuna sai sun durkusar da su.
Buhari ya yi gargadin cewa gwamnatin sa ba zata taba barin wata kungiya ta durkusar da kasar ba sannan kuma su halaka rayukan mutane ba tare da ta dauki mataki ba.
KU KARANTA KUMA: Ekiti: PDP za ta yi zanga-zangan lumana na gama gari
Shugaban kasar ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati, iyalan wadanda abun ya shafa da kuma mutanen jihar Sokoto, inda ya bayyana harin a matsayin rashin imani.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng