Ga dukkan alamu Saraki ne ya kafa wannan kungiyar ta 419 da ake kira da R-APC – Sanata Adamu
Abdullahi Adamu, sanata mai wakiltan Nasarawa na yamma a majalisar dattawa, ya bayyana sabuwar APC (R-APC) a matsayin kungiyar yan damfara.
A wata hira da manema labarai a hedkwatan APC dake Abuja, dan majalisan ya ce ga dukkan alamu shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya kafa kungiyar.
Ya ce babu wani dan kungiyar sabuwar Peoples Democratic Party (PDP) da ya amfana daga gamayar kungiyar kamar Saraki amma duk da haka shugaban majalisar dattawa ya nuna butulci ga APC.
KU KARANTA KUMA: Ekiti: PDP za ta yi zanga-zangan lumana na gama gari
Ya bayyana kungiyar a matsayin na jabu, sannan kuma cewa baya tunanin jam’iyyar zata zamo barazana ga jam’iyyar a zabe mai zuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng