Yanzu Yanzu: An kashe mutane da dama, sannan an sanyawa gidaje da dama wuta yayinda wasu yan bindiga suka kai hari kauyukan Sokoto
Wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kai hari kauyuka dake kewayen Gandi a karamar hukumar Rabah dake jihar Sokoto, inda suka kashe wasu mutane da ba’a bayyana adadinsu ba sannan kuma suka kona gidaje da sauran kayayyaki.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa mazauna yankin da suka rayu a hare-haren na nan sun zama marasa galihu a yanzu.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandar jihar, Cordelia Nwewe, ya tabbatar da lamarin.
Nwewe ya ce kwamishinan yan sanda na jihar, Muritala Mani, da jami’an lafiya sun tafi karamar hukumar domin duba yanayin da lamarin ke ciki da kuma duba yawan mutanen da abun ya shafa.
KU KARANTA KUMA: Sa’o’i 24 bayan shiga yarjejeniya, PDM, da wasu 19 sun nisanta kansu da Maja
Ya kara da cewa za’a ji Karin bayani da zaran kwamishinan yan sandan ya dawo.
Nwawe ya ce ana nan ana ci gaba da bincike.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng