Yanzu Yanzu: El-Zakzaky, da matarsa sun isa kotu cike da matakan tsaro

Yanzu Yanzu: El-Zakzaky, da matarsa sun isa kotu cike da matakan tsaro

Shugaban kun giyar Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat sun isa babban kotun jihar Kaduna idan za’a gurfanar da su cike da matakan tsaro a ranar Laraba.

Gabannin gurfanar da sun, jami’an yan sandan jihar Kadun a sun toshe dukkanin hanyoyin dake sada mutane da kotun, inda suke karkatar da ababen hawa zuwa saurfan hanyoyi.

A cewar yan sandan, an yi wannan yunkuri ne domin hana yan kungiyar shi’a dake zanga-zanga da dama na a saki shugabansu a Kaduna da Abuja karya doka.

Mazauna yankin da wuraren aikinsu ke ta hanyar da daliban makaranta da suke kusa da kotun na tafiya ne a kafa zuwa inda za su sakamakon cunkoson motoci da aka samu a yankin.

Yanzu Yanzu: El-Zakzaky, da matarsa sun isa kotu cike da matakan tsaro

Yanzu Yanzu: El-Zakzaky, da matarsa sun isa kotu cike da matakan tsaro

Gwamnatin jihar Kaduna ce ta gurfanar da El-Zakzaky da matarsa Zeenat a gaban koton jihar.

KU KARANTA KUMA: Sa’o’i 24 bayan shiga yarjejeniya, PDM, da wasu 19 sun nisanta kansu da Maja

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar dattawa za ta yi mahawara kan ci gaba da tsare tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Sambo Dasuki da shugaban kungiyar Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Sanata David Umaru (APC, Niger) na cikin wadanda ya kamata suyi muhawara kan takardan a jiya, amma aka dage saboda rashin bayyanan sanatan a zauren.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel