Real Madrid za ta nemi Hazard, Neymar ko Mbape bayan tashin Ronaldo

Real Madrid za ta nemi Hazard, Neymar ko Mbape bayan tashin Ronaldo

Mun ji labari cewa ta tabbata babban ‘Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya tashi ya koma Kungiyar Juventus ta kasar Italiya bayan yayi shekaru kusan 10. Yanzu dai an fara maganar wadanda ake sa rai za su maye wurin ‘Dan wasan.

Real Madrid za ta nemi Hazard, Neymar ko Mbape bayan tashin Ronaldo

Watakila Neymar Jr. ya karbe wurin Ronaldo a Real

Daga cikin manyan ‘Yan wasan da ake sa rai za su maye wurin tsohon ‘Dan wasan Real Madrid Ronaldo da ya ci kwallaye sama da 450 a cikin shekara 9 akwai babban ‘Dan wasan gaban Brazil Neymar da kuma Takwaran sa na Kungiyar PSG.

KU KARANTA: An haifawa Shugaban kasa Buhari jika a Sifen

1. Neymar Jr.

Ba mamaki Real ta nemi tsohon ‘Dan wasan gaban Barcelona Neymar Jr. ya toshe kafar da Ronaldo ya bari. Tun Neymar yana karamin yaro Real ke sha’awar ‘Dan wasan da yanzu ya fi kowa tsada a Duniya wanda yanzu yake PSG.

2. Eden Hazard

Akwai yiwuwar Real Madrid ta yi kokarin sayen ‘Dan wasan gaban nan na Kasar Belgium Eden Hazard. Hazard wanda kwanan nan aka cire kasar sa daga Gasar cin kofin Duniya yana takawa Kungiyar Chelsea ta Ingila leda ne a halin yanzu.

3. Kylian Mbape

Tun a bara aka yi tunani Real Madrid za ta nemi ‘Dan wasan gaban nan Kylian Mbape. Matashin ‘Dan kwallon ya koma PSG ne a matsayin ‘Dan kwallon aro kafin a saye sa bana kan kudi masu tsada kuma ba mamaki don ya dawo Kasar Sifen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel