Direban da yayi gangancin kashe wasu mutane 3 masu tafiya a gefen hanya ya gurfana gaban alkali
- Sauri ya haifi nawa bayan da wani direba yayi awan gaba da wasu mutane
- Wanda tafiyar ruwan da yayi da su kuma ya zama sandiyyar mutuwarsu
A ranar Litinin ne aka gurfanar da wani direba mai suna Tijani Basit a gaban babbar kotun majistire da ke birnin Abeokuta bisa zarginsa da yin tukin ganganci wanda hakan ya yi sanadiyar kashe mutane har 3.
Direban mai kimanin shekaru 42 da haihuwa yana fuskantar tuhumar aikata laifuka guda biyu wadanda su ka hada da tukin ganganci tare kuma da rashin lasisin tukin Mota.
KU KARANTA: ‘Yan uwa 2 sun fada tarkon masu garkuwa da mutane, an nemi Naira miliyan N15m kudin fansa
Dan sanda mai gabatar da kara ASP Sunday Eigbejiale, ya bayyanawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a yankin Alapako da ke kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan, a ranar 2 ga watan Yuli nan da muke ciki da misalin karfe biyu na rana.
Ya kara da cewa Basit ya tuko motarsa ne kirar Toyota Camry cikin tsananin gudu, dalilin hakan ne ya sanya kasa sarrafa motar tasa wanda nan take ya kashe wasu mutune 3 da su ke tafiya a gefen hanya.
A karshe kotun ta dage sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Augusta mai zuwa tare kuma da bayar da belin wanda ake zargin akan kudi kimanin Naira miliyan daya N1m hadi da shaidu guda biyu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng