Mambobin R-APC na majalisar dokoki na shirin yiwa APC kankat a ranar 31 ga watan Yuli

Mambobin R-APC na majalisar dokoki na shirin yiwa APC kankat a ranar 31 ga watan Yuli

Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress a majalisar dattawa da na majalisar wakilai na iya komawa jam’iyyar Peoples Democratic Party kafin ranar 31 ga watan Yuli, kamar yadda majiyarmu ta Sunday Punch ta ruwaito.

An tattaro cewa kungiyar sabuwar APC ta rabu daga ainahin jam’iyyar APC mai mulki a ranar Laraba da ta gabata sannan kuma an kawo cewa suna shirye-shirye barin jam’iyyar a tawaga mai yawa.

Za’a maimaita irin yadda yan sabuwar PDP suka sauya sheka zuwa APC a gabannin zaben 2015 cikin shekarar 2014.

Mambobin R-APC na majalisar dokoki na shirin yiwa APC kankat a ranar 31 ga watan Yuli
Mambobin R-APC na majalisar dokoki na shirin yiwa APC kankat a ranar 31 ga watan Yuli

Hakan na faruwa ne sakamakon zargin da mambobin jam’iyyar ke yi na ganin cewa an mayar da su saniyar ware bayan da su ne aka kafa jam’iyya mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Yadda Najeriya za ta ci gaba da dorewa – Obasanjo

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa wasu shugabannin gamayyar jam’iyyar mai mulki, APC, a ranar Litinin sun hadu a Abuja domin jiga yarjejeniya da wasu jam’iyyun adawa kan zaben 2019.

Mambobin kungiyar sabuwar APC (R-APC) karkashin jagorancin shugabansu Buba Galadima sun halarci taron a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng