Maganganun ‘Dan Majalisar Jihar Filato sun bar baya da kura

Maganganun ‘Dan Majalisar Jihar Filato sun bar baya da kura

- Wani ‘Dan Majalisa ya zargi ‘Yan siyasa da hannu cikin rikicin Jihar

- Kalaman Ahmad Wase da ke wakiltar Yankin Filato sun kawo sabani

- Wasu manyan ‘Yan Majalisa a Jihar sun karyata Hon. Ahmad I. Wase

Mun samu labari daga babban Birnin Tarayya Abuja cewa ‘Yan Majalisar da ke wakiltar Jihar Filato a Majalisar Wakilan Tarayya sun samu sabani bayan da wani yayi ikirarin cewa akwai hannun ‘Yan siyasan Jihar a rikicin da ake yi.

Maganganun ‘Dan Majalisar Jihar Filato sun bar baya da kura
Sanata Jonah Jang yace babu hannun 'Yan siyasa a rikicin Jos

Ahmed Idris Wase yayi wani jawabi a wancan makon lokacin da ya mike a Majalisar inda ya zargi wasu manyan ‘Yan siyasa da hannu cikin rikicin Filato. ‘Dan Majalisar yace akwai wasu mutane da aka horar da makamai a wajen kasar.

Honarabul Wase ya zargi Jami’an tsaro da sakaci wajen aikin su inda yace binciken da su kayi a baya ya tabbatar da cewa an horar da wasu mutane kimanin 300 a Kasar Israila wanda kuma har yau babu wanda ya san inda su ke.

KU KARANTA: Mai kudin Afrika Dangote zai kashe Miliyoyin kudi a Garin Shugaban Kasa

Sai dai wasu ‘Yan Majalisar da ke wakiltar Jihar Filato a Majalisar Tarayya sun ce Honarabul Ahmad Wase ba gaskiya yake fada ba. Sanatocin Jihar Filato irin su Jonah Jang da Jerry Husseini tuni su ka karyata ‘Dan Majalisar.

Haka-zalika sauran ‘Yan Majalisar Wakilan Jihar Filaton ba su amince da abin da Takwaran na su ya fada ba, Gyang Pwajok, Johnbull Shekarau, Timothy Golu da Solomon Maren duk sun ce ‘Dan Majalisar ba zaman lafiya ya ke nema ba.

Kwanaki rikicin Makiyaya da Birom ya barke a Garin Filato wanda ta sa dole Sufetan ‘Yan Sanda ya aika Runduna guda zuwa Garin Jos domin ganin an kawo zaman lafiya. Shugaba Buhari dai yace akwai hannun 'Yan siyasa a lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng