2019: Matasan Arewa sunce basu yadda shugaba Buhari ya zarce ba

2019: Matasan Arewa sunce basu yadda shugaba Buhari ya zarce ba

A ranar Litinin dinnan ne Shugabannin Matasan Arewa suka ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai canci a bashi damar fitowa takara a karo na biyu ba

2019: Matasan Arewa sunce basu yadda shugaba Buhari ya zarce ba
2019: Matasan Arewa sunce basu yadda shugaba Buhari ya zarce ba

A ranar Litinin dinnan ne Shugabannin Matasan Arewa suka ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai canci a bashi damar fitowa takara a karo na biyu ba. Da suke magana akan tsayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da 'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka yi na yankin Arewa masu Yamma a Kaduna, daya daga cikin shugabannin kungiyar matasan arewan, Alhaji Gambo Gujungu, yace shugaban kasar bai cancanci a bashi damar fitowa takara a karon na biyu ba.

DUBA WANNAN: Muna da kwararan shaidu akan hannun 'yan siyasa a rikicin dake faruwa a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

Gujungu yace bayan irin kashe - kashen da ake yi a fadin kasar nan, musamman ma a yankin arewa, Buhari zai yi shekaru hudu ne ya hakura da mulki domin wani dan arewa ya samu. Gujungu yace ya fahimci cewa shugaban kasar yana dora alhakin kashe - kashen da ake yi a kasar nan akan wasu 'yan siyasa da har yanzu ba'a bayyana ko suwaye ba.

Ya ce 'yan Najeriya su dora dukkan laifin abinda ke faruwa a kasar nan akan shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin ya bayyana wa jama'a cewa wasu 'yan siyasa ne suke da hannu a cikin kashe-kashen wadanda har yanzu bai bayyana ko suwaye ba. Saboda haka muna kira gare shi daya bayyana 'yan siyasan da suke da hannu a wannan rikicin dake faruwa a kasar nan.

A ranar Lahadin nan ne wasu 'yan jam'iyyar APC na jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara suka nuna goyon bayan su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a zabe mai zuwa na shekarar 2019. Sun bayyana cewa shugaban kasar yayi kokari sosai wurin yaki da ta'addanci, cin hanci da rashawa, da kuma wasu muhimman cigaba a kasar nan, saboda haka ya kamata a bashi dama ya fito a karo na biyu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel