Saboda tsananin hidimtawa Buhari da nayi, sau 38 ana kulle ni – Buba Galadima
- Yadda na wahaltawa Buhari duk na kusa da shi ba su wahalta masa kamar haka ba
- Mafi yawancin makusantan Buhari na yanzu 'yan ciranin siyasa ne
- Wani tsohon makusancin Shugaba Buhari ne ya bayyana haka
Shugaban tsagin sabuwar Jamiyyar APC mai lakabin rAPC Alhaji Buba Galadima, ya bayyana yadda abubuwa su ka same shi a dalilin shugaban kasa Muhammad Buhari.
Buba Galadima wanda tsohon makusancin shugaban kasa Buhari ne, ya bayyana cewa sau 38 ana garkame shi akan yana tare da Muhammadu Buhari, ya kara da cewa sau 5 ana yi masa tayin mukamin Minista amma yayi biris da tayin.
Ya fadi hakan ne a lokacin da ya bakunci wani shiri da gidan talabijin na AIT yake a gabatarwa a kowacce Asabar.
Sannan ya kuma ce yanzu wadanda su ke cikin gwamnatin shugaba Buhari yan ta fadi gasassa ne, domin 'yan ciranin siyasa ne.
"Bani da wata matsala da Shugaba Buhari, domin kuwa tun daga watan janairun Shekarar 2002 na ke taimakonsa akan ya zama shugaban kasa. Domin na ba shi gudummawar da ko shi kan sa bai baiwa kansa ba, kuma babu wani dan kasar nan da zai iya wannann sadaukarwar" in ji Buba Galadima.
KU KARANTA: Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya da su cigaba da bada hadin kai wajen yaƙar cin hanci da rashawa
Ya cigaba da cewa, "A dalilin shugaba Buhari na fuskanci tuhuma, dauri da kuma cin zarafi, kai har daure ni aka yi sau 38, amma hakan bai tsaya iya nan ba, domin kuwa har daure ne aka yi tamau tare da garkameni".
A karshe kuma ya bayyana takaicinsa dangane da yadda wasu mutane su ka kewaye shugaba Buhari, wadanda a baya su ne suke bayar da kudi domin ganin burinsa na mulkin kasar nan bai kai ga nasarar ba.
Da ya ke bayani a kan dangantakarsu da shugaba Muhammad Buhari bayan an kammala zaben 2015, ya ce jim kadan da kaiwa ga nasarar zaben, sai shugaba Buhari ya yi taro da manema labarai na duniya, inda ya bayyana cewa ba shi da bukatar kuri'ata da ta magoya bayana da ta kuma iyalina da ma ta sauran duk wanda ya ke tare da ni.
A karshe Buba Galadima ya tofa albarkacin bakin sa akan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin shugaba Buhari ta keyi, inda ya ce;
"Wannan yana a matsayin wasa da Hankalin ne kawai, ya kamata gwamnati da ta sauya fasali da tsarin yadda ta ke yi akan yaki da cin hanci da rashawa"
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng