Jami’o’i 11 zasu yi watandar tallafin Naira N84m

Jami’o’i 11 zasu yi watandar tallafin Naira N84m

- Gwamnati ta yunkuro don habbaka bangaren ilimi

- Yanzu haka jami'o'i da yawa ne zasu amfana da wani tallafi da gwamnatin zata bayar

- Kudin zasu yi amfani da su ne domin yin wasu muhimman aiyuka

Jami'o'i 11 ne za su amfana da Naira miliyan N84m da gwamnatin tarayya za ta raba domin zurfafa bincike.

Jami’o’i 11 zasu yi watandar tallafin Naira N84m
Jami’o’i 11 zasu yi watandar tallafin Naira N84m

Tun da farko dai manufar asusun shi ne samar da kudi domin bincike akan ma'adanai wadanda su ke cikin ruwa da tono su, da na cikin kasa da kuma ma'adinan da ke cikin ruwa.

Mai rikon Mukamin Ministan Ma'adinai da tama na kasa Abubakar Bwari ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke mika takardun amincewa ga wakilan jami'ar a Abuja.

"Wannan gwamnatin ta samar da yanayin mai kyau yadda masu zuba jari za su zuba jari domin cigaban kasar nan" inji ministan.

KU KARANTA: Zaɓen jihar Ekiti: Hukumar zaɓe ta ƙasa ba ta raba kayan aiki a wasu ƙananan hukumomi ba

Jami'o'in da za su amfana da wannan kudin sun hada da Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife da jami'ar fasaha ta gwamnatin tarayyaa da ke Minna da jami'ar Najeriya da ke Nsukka da kuma jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Sauran sune Jami'ar Ibrahim Babangida da ke jihar Niger, wacce za ta rabauta da Naira miliyan N9m.

Sai kuma jami'ar fatakwal da ta Jos, da ta Legas da kuma jami'ar Ibadan, da Jami'ar jihar Nasarawa da ta jihar Ebonyi da za su rabauta da sama da Naira miliyan N6m.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng