Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin taron bikin ranar sojoji (hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin taron bikin ranar sojoji a Monguno jihar Borno a ranar Juma’a, 6 ga watan Yuli.
Shugaban kasar ya kasance tare da ministan tsaro Monsur Dan Ali, Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, babban hafsan soji, Laftanal Tukur Yusuf Buratai da kuma Manjo Janar Olabanji.
Shugaban kasar ya kaddamar da ‘ARA’ makaman yaki masu sulke wanda aka kera a gida a lokacin taron.
KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Borno Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Borno
A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Borno a yau Juma'a. Gabanin zuwansa, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya rigayesa da zuwa jihar Borno a jiya domin ganewa idonsa yadda ake shirye-shriyen bikin da kuma ziyara ga yan sansanin gudun hijra a jihar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng