Cututtuka 5 da abarba ke magani
Kayan marmari na da matukar amfani a jikin Dan Adam, ta hanyar basa kariya daga cututtuka sannan kuma ya karama garkuwar jiki kuzari.
Daga cikin abubuwan marmari dake da wannan alfanun akwai abarba, don haka muka kawo maku wasu daga cikin waraka da shan sa ke yi.
Ga magunguna 5 da abraba ke yi:
1. Abarba na maganin cutar nan ta atiraitis mai damun gabbai da jijiyoyi inda su ke kumbura har su hana mutum sakat. Yawan shan abarbara na maganin wannan ciwo.
2. Abarba na maganin cutar daji wato ‘kansa’ mai lahanta kwayoyin garkuwa saboda sinadarin da ya kunsa na bitamin A da C da sauran su .
3. Abarba na magananin sanyi da mura idan aka yawaita shan sa saboda yana tattare da wasu sinadarai da ke kashe majina.
4. Hawan jini Abarba na kare cutar hawan jini saboda sindarin ‘Pottasium’ da take dauke da shi mai amfani wajen yawo da jini a jikin mutum.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa Adamu Ciroma rasuwa yana da shekara 84
5. Abarba na hana tsufa baya ga gyara idanu ya kuma kare mutum daga irin cutar dimuwa da sauran cututtuka na tsufa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng