An kashe dan gidan shugaban ISIS Al-Baghdadi a harin Amurka

An kashe dan gidan shugaban ISIS Al-Baghdadi a harin Amurka

- ISIS ita ta kafa daular Islama a Iraki da Siriya

- Ta kashe jama'a da yawa ta bautar da wasu da sunan shari'a

- Yanzu kam kasar Siriya da Amurka da Iraki sun hada kai sun fatattake su

An kashe dan gidan shugaban ISIS Al-Baghdadi a harin Amurka
An kashe dan gidan shugaban ISIS Al-Baghdadi a harin Amurka

Kungiyar mayakan IS ta ce an kashe Hudayfah al-Badri dan shugabanta, Abu Bakr al-Baghdadi a wani hari da aka kaddamar a Syria.

Kafar yadda farfagandar kungiyar ta Amaq ta ce an kashe shi ne a wani hari da aka kai, kan wata cibiyar wutar lantarki da ke birnin Homs.

Tun bayan da kungiyar ta kafu a kasar Iraqi da Siriya suke ta'addancinsu yadda suke so, kamar kamawa dda sayar da bayi, kisa dacsunan jihadi, da ma shariar Islama tsantsa, wadda a zamanin nan take tayar da hankulan mutane.

DUBA WANNAN: Matsalar Najeriya tafi karfin Faransa

A kokarin su na tserewa uqubar Buhari, a 2015, kungiyar Boko Haram ita ma tayi mubayi'a ga Al-Baghdadi, sai dai shi kuma Al-Baghdadi, wanda yace shi jikan annabi ne, ya sauke Shekau daga shugabanci, ya dora dan gidan Muhammad Yusuf, lamari a ya raba kan kungiyar a 2016.

Mayakan ISIL da Boko Haram, Alshabab da na Alqaida, na Ansaru da na Taliban dai, duk daga Addinin Islama aka samo su, bangaren Sunni, inda su kuma Shia suka samar da na Hizbulla da masu biyayya ga Zazzaki a Najeriya da Labanon.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel