Matsalar Tsaron kasarku tafi karfin kasar Faransa ta magance muku - Shugaba Macron
- Shugaba Emmanuel Macron, na kasar Faransa yace kasar shi bazata iya tallafawa Najeriya da Afirka ba, ta fannin tsaro
- Mista Macron yace, domin shawo kan matsalar, Gwamnatocin kasashen Afirka ne ya kamata su hada kansu don kawo karshen 'yan jihadi'
- Shugaban yayi wannan maganar ne a taron hadin guiwa na yan jaridu da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan tataunawar su a fadar shugaban kasar dake Abuja
Shugaba Emmanuel Macron, na kasar Faransa yace kasar shi bazata iya tallafawa Najeriya da Afirka ba, ta fannin tsaro.
Mista Macron yace, domin shawo kan matsalar, Gwamnatocin kasashen Afirka ne ya kamata su hada kansu don kawo karshen 'yan jihadi'
Shugaban yayi wannan maganar ne a taron hadin guiwa na yan jaridu da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan tataunawar su a fadar shugaban kasar dake Abuja.
Bada amsar tambayar da aka yi wa shugaban Faransan akan taimakon da kasar shi zata iya ma Najeriya wajen yaki da kalubalen rashin tsaro dake addabarta.
Macron yace "Da farko dai, a tunani na wannan tsarin na Afirka ne kuma Faransa bazata iya shawo kan matsalar halin da Afirka ke ciki ba."
DUBA WANNAN: 1% na jama'ar Najeriya ke karatun jami'a
"Amma abinda zamu iya shine shiga cikin al'amarin Afirka domin yaki da ta'addanci balle a kasar Mali da yankin ta. Zamu kuma zauna tare da su iya tsawon da kawayen namu suka bukata ballantana kasar Mali, kamar yanda muka tattauna jiya (litinin) akan wannan matsalar."
"Amma abu mafi muhimmanci gareni shine yanda mabanbantan gwamnatocin Afirka zasu tsara yanda zasu yi yaki da ta'addanci da kuma kawo karshen 'yan'ta'addan jihadi." yace.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng