Sallamar Malamai: Gwamnatin jihar Kaduna ta gayyaci mutane 20,000 cikin 51,000 masu neman aikin koyarwa

Sallamar Malamai: Gwamnatin jihar Kaduna ta gayyaci mutane 20,000 cikin 51,000 masu neman aikin koyarwa

Gwamnatin jihar Kaduna ta karkashin jagorancin ma'aikatar Ilimi ilimin ta gayyaci masu neman aikin koyarwa 20,000 domin yi musu gwajin gaba da gaba.

Za ku tuna cewa gwamnatin jihar ta sallami malaman makaratu 21,000 a bara sanadiyar fadi jarabawar gwaji da akayi musu. Gwamnatin ta yi alkawarin cewa za ta dauki sabbin malami 25,000.

Zuwa yanzu, gwamnatin jihar ta dauki malamai 10,000 wanda aka karawa albashi domin janyo hankalin matasa aikin koyarwa.

Sallamar Malamai: Gwamnatin jihar Kaduna ta gayyaci mutane 20,000 cikin 51,000 masu neman aikin koyarwa
Sallamar Malamai: Gwamnatin jihar Kaduna ta gayyaci mutane 20,000 cikin 51,000 masu neman aikin koyarwa

Gwamnatin jihar ta bayyana wannan ne a wani jawabi da saki inda ta ce:

"Hukumar Ilimi ta Bai-Daya ta Jihar Kaduna jiya Talata 3/06/2018 ta fara gwaji ta hanyar ganawa da masu neman aikin koyarwa a makarantun firamare a kokarin da hukumar ke yi na daukan sababbin kwararrun malamai 11,000 don cike gurbin malamai 25,000 da za ta dauka.

Yanzu haka Hukumar SUBEB ta gayyaci mutum 20,000 cikin 51,000 da suka yi nasara a jarrabawar da aka yi don daukan kwararrun malamai a kashi na biyu.

Don haka hukumar na kara gargadin cewa a yi hankali da 'yan damfara masu yawo suna damfarar mutane cewa za su ba su aiki. Don haka duk in aka ci karo da irin wadannan 'yan damfarar a taimaka a sanar da hukuma don su fuskanci hukunci."

KU KARANTA: El-Rufa’I ya samar da dokan da ka iya garkame yan Shi’a da wasu na shekara 7 a kurkuku

Gwamnan jihar ya dauki alwashin cewa zai habaka ilimi a makaratun gwamnatin jihar duk da cewa wasu na sukarsa akan wannan kudiri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel