Hikima: Yadda wani fasihin Yaro ya burge shugaban kasar Faransa da sana’arsa (Hotuna)
Wani dan kamarin yaro dan shekaru 11 mai cike da basira, hikima, fasaha sakamakon wata baiwa da Allah ya yi masa ya baje kolinsa fasaharsa a gaban shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron a jihar Legas, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru,NAN, ta nuna.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yaron mai suna Kareem Olamilekan na da tsananin zanen abubuwa kamar su yi magana, don haka aka gayyace shi taron da gwamnatin jihar Legas ta shirya ma shugaban Faransa, Emmanuel Macro a yayin ziyarar da ya kai shelkwatar mawakin Najeriya, Fela, Afrika Shrine.
KU KARANTA: Babban dalilin da yasa n adage lallai sai na kai ziyara jihar Legas – Shugaban kasar Faransa
Haka kuwa aka yi, inda a yayin wannan taro Kareem ya nade hannu ya fara aikin zana Macron a yadda yake a wannan lokaci, inda cikin dan kankanin lokaci da bai wuce awanni biyu ba har ya zana shugaban cikin wani hoto mai matukar kyau.
Kwarewar wannan yaron ta sanya Macron yaba masa, tare da gode masa kwarai da ya zana shi, a shafinsa na Twitter, inda yace; “Basirar wannan yaron ta taba ni, barka da wannan Yaro.”
Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro akwai mai gayya mai aiki, Gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode, Sanata Ben Murray Bruce, Farfesa Wole Soyinka, shahararrun yan Fim din Nollywood, Olu Jabos, da Joke Silva.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng