Kowa ya sani idan Buhari ya dauki ra’ayi ya dauka kenan, baya jin shawara -Inji Gumi

Kowa ya sani idan Buhari ya dauki ra’ayi ya dauka kenan, baya jin shawara -Inji Gumi

Fitaccen Malamin addinin Islama, Dakta Ahmed Gumi ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya jin shawara, don kuwa idan ya dauki ra’ayi ya dauka kenan, a cewarsa ba yau ya fara mu’amala da Buhari ba.

Dakta ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da gidan rediyon BBC Hausa, inda suka tuntube shi akan menene dalilin haduwarsa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a wani hoto dake yawo, kuma dame dame suka tattauna.

KU KARANTA: Auren soyayya ya mutu sakamakon musun kan wanda ya fi tsakanin Ronaldo da Messi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daktan yana fadin wannan hoto an dauke shi ne a wani lokaci a baya yayin wani daurin aure da suka halarta a garin Kaduna tare da wani tsohon gwamna, inda yace: “Bayan mun yi gaishe-gaishe, sai na fada ma Atiku Abubakar cewa akwai wani daurin aure da muka hadu da ni da shi, aka dauki hotonmu da ni da shi da wani tsohon gwamna

Kowa ya sani idan Buhari ya dauki ra’ayi ya dauka kenan, baya jin shawara -Inji Gumi
Atiku da Gumi

“Sa’annan na fada masa cewa jama’a sun ce tun dai har an gan mu tare da ni da shi da wancan tsohon gwamnan, to na zama dan PDP kenan” Inji shi, sai dai Daktan yace a lokacin da aka dauki hoton Atiku ma APC.

Haka zalika Daktan ya koka kan yadda a duk lokacin da mutane suka gan shi tare da wani dan siyasa, a maimakon su kyautata masa zato, yawancinsu munanan zato suke masa, amma fa yace ba zai taba yin shiru ba game da duk abinda zai cuci Jama’a ko addini.

Sai dai da aka tambayeshi ko ya taba neman Buhari da kansa ya bashi shawara, sai yace “Kowa ya san halinsa, idan ya dauki ra’ayi ya dauka kenan, idan ba mashawarcinsa ba, ba yau ya fara mu’amala da shi ba.”

Daga karshe ya tabbatar da cewa sukar mai suka ba zai sanya shi yin shiru akan duk abinda zai cuci jama’a ba, inda yace maganganun da yayi a lokacin tsohuwar gwamnatin da ta shude sun fi zafi akan wanda yake yi, “Alhalin cutarwar da ake yi ma yan Najeriya a wannan gwamnati ya fi wanda aka yi musu a baya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng