Duk wanda ya taba Shugaba Buhari ya tabo tsuliyar dodo – Ndume

Duk wanda ya taba Shugaba Buhari ya tabo tsuliyar dodo – Ndume

- Ali Ndume na Jam’iyyar APC yace Shugaba Buhari na da farin jini

- Sanatan APC yace duk wanda ya taba Buhari ya jawowa kan sa aiki

- ‘Dan Majalisar ya tabbatar da cewa akwai matsaloli amma ana gyara

‘Dan Majalisar Dattawan da ke wakiltar Yankin Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume yayi hira da manema labarai inda yayi magana game da irin farin jinin da Shugaban kasa Buhari yak ke da shi.

Duk wanda ya taba Shugaba Buhari ya tabo tsuliyar dodo – Ndume
Sanata Ali Ndume yace Shugaba Buhari ya mori farin jini

Mun samu labari cewa babban Sanatan APC Ali Ndume ya bayyana cewa duk wanda yayi gigin sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasuwa to sai dai a haifi wani kuma ba shi ba saboda kaunar da jama’a su ke yi masa.

KU KARANTA:

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Sanatan na Borno ya bada misalin yadda Jama’a su kayi watsa-watsa da Charly Boy lokacin da yake kokarin yi wa Gwamnatin Buhati zanga-zanga a kasuwar Wuse da ke Birnin Tarayya Abuja.

Jama’a dai sun dura kan Charly Boy ne lokacin da ya ke zanga-zangar sa inda ta sa dole ya tsere daga kasuwar. Bayan nan ‘Dan Majalisar ya bayyana cewa akwai matsaloli a APC saboda hadakar da aka samu na Jam’iyyu iri-iri.

Sanatan ya bayyana cewa masu sukar Gwamnatin nan su ne su ka kashe Najeriya na tsawon shekaru inda yace Shugaba Bhari na bakin kokarin sa wajen cika manyan alkawuran da ya daukarwa ‘Yan Najeriya lokacin neman zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng