Hattara dai! gwamnatin jihar Kaduna ta bullo da wata hanyar kawar da yan sara suka
A kokarinta na magance matsalar tsaro musamman wanda ta shafi ayyukan yan sara suka, yan daba da yan shara, Gwamnatin jihar Kaduna ta Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta bullo da wata sabuwar doka da ta tanadi hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari ga duk dan daba, sara suka ko dan shara.
Babban lauyan gwamnatin jihar, Chris Umar ne ya sanar da haka a ranar Talata, 3 ga watan Yuli a yayin wani taron ganawa da manema labaru, inda yace dokar ta fara aiki ne tun daga ranar 27 ga watan Yuni.
KU KARANTA: Yan Mata 4 sun gamu da ajalinsu a cikin wani madatsar ruwa na jihar Katsina
“Dokar ta haramta duk wasu kungiyoyin yan daba, sara suka da yan shara da suke addabar al’umma, tare da lalata zaman lafiya a tsakanin mutane, ta hanyar sace sace, fashi da makami, kashe kashe da kuma fyade.
“Da wannan ne gwamna jihar Kaduna ya yi amfani da damar da sashi na 45 (1) na da 5 (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya suka bashi, inda ya haramta duk wani kungiya dake tayar da hankulan jama’a da kuma yi ma doka karantsaye.” Inji shi.
Umar ya cigaba da cewa: “An sha kama yan sara suka a baya, amma sai cikin kankanin lokaci kaga an sako su, har ma su koma suna cigaba da ayyukansu na ta’addanci, tare da farautar duk wanda suke ganin shine ya kai rahotonsu ga hukuma, don haka wannan sabuwar doka ta magance wannan.”
Daga karshe yace kasancewa dan wannan kungiya ko da baka taba aikata laifi ba ya isa a kama mutum, kuma shima hukuncin ya shafeshi, don haka ya yi kira ga iyaye dasu ja hankulan yayansu, tare da nushesu matsalar sara suka ga rayuwarsu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng