Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari ya nuna tsantsar soyayya ga yan Igbo – Rochas Okorocha

Shugaba Buhari ya nuna tsantsar soyayya ga yan Igbo – Rochas Okorocha

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayya cewa yan kabilar Igbo na son Buhari.

Abubuwan da yake yi a kasar Igbo ya taba zakatansu. Cewa ya san da yan Igbo na son sa sannan sun yi kazamar siyasa a 2015, saboda basu yi imani da Buhari ba amma zasu zabe shi sosai a 2019.

Ya bayyana hakan a wani babban gangamin APC a Kudu maso gabas mai taken gangamin APC don Buhari wanda aka gudanar a dakin wasa na Dan Anyiam Owerri a ranar Talata.

Shugaba Buhari ya nuna tsantsar soyayya ga yan Igbo – Rochas Okorocha

Shugaba Buhari ya nuna tsantsar soyayya ga yan Igbo – Rochas Okorocha

Da yake Magana ta bakin babban sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Gida Mustapha Buhari ya bayyana cewa mutanen kudu maso gabas da yan Igbo na da damar shugabanci kasar tunda suma yan kasa ne.

KU KARANTA KUMA: Wani kwamitin je-ka-nayi-ka ta dakatar da ni daga Majalisar Dattawa - Sanatan APC

Buhari ya kuma bayyana cewa zasu mara masu baya a duk lokacin da hakan ya ya taso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel