Wani barawo ya gamu da hukuncin kisa ta mummunar hanya bayan ya yi ma Yansanda fashi da makami

Wani barawo ya gamu da hukuncin kisa ta mummunar hanya bayan ya yi ma Yansanda fashi da makami

Dubun wani matashin dan fashi da makami, Abdulateef Babatunde ta cika a ranar da ya tare wasu jami’an Yansanda guda biyu, a garin Ado Ekiti, inda ya kwace musu baburansu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

A ranar Litinin, 3 ga watan Yuli ne babbar kotun jihar Ekiti dake sauraron karar da aka shigar da barawon ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta kama shi da aikata laifuka biyu da ake tuhumarsa dasu.

KU KARANTA: Fulani makiyaya sun ci wasu Inyamurai taran naira miliyan 2 saboda kashe musu shanu

A ranar 16 ga watan Yunin shekarar 2016 ne dan fashin ya tare wani dansanda mai suna Babatimilehim Kayode akan babur dinsa mai lamba GED 550 QA, ya bukace shi ya nuna masa tikitin shaidar biyan haraji, inda Dansanda ya fada masa shi fa dansanda ne ba dan achaba ba.

Sai dai dan fashin bai dandara ba, nan take ya nuna ma Dansandan bindiga, ya umarce shi ya sauka ya bashi babur din ko kuma ya kashe shi, ba tare da musu ba, Dansandan ya sauka, amma daga bisani ya yi masa ihun barawo, inda jama’a suka yi masa tara tara, aka kama shi.

Haka zalika a wani lokaci na daban, dan fashin ya taba tare wani jami’an Dansanda na daban, mai suna Sheidu Ganiyu, shi ma yana kan babur dinsa kirar Bajaj, inda ya bukaci Dansandan ya rage masa hanya, amma a yayin da suke kan hanya sai ya nemi da ya tsaya ya sauke shi, saukarsa ke da wuya sai ga wasu mutane uku sun fito daga daji suka nuna masa bindiga, suka kwace masa babur.

A yayin shari’ar, lauya mai kara ya bayyana ma Kotu babur din Dansanda Ganiyu, tare da wata bindiga da dan fashin ke amfani da ita wajen aikinsa.

Da yake zartar da hukunci, Alkali Omotoso ya bayyana cewa laifin Babatunde ya saba ma sashi na 402 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Ekiti, inda ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, daga karshe kuma yayi fatan Allah ya jikansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel