Sun fito da ransu bayan sun shafe kwanaki 9 babu abinci a kogon dutse

Sun fito da ransu bayan sun shafe kwanaki 9 babu abinci a kogon dutse

An gano wadansu yara 'yan wasan kwallon kafa su 12 da kocinsu, bayan sun shafe kwanaki 9 a cikin wani katon kogon dutse wanda yake dauke da ruwa a kasar Thailand

Sun fito da ransu bayan sun shafe kwanaki 9 a kogon dutse ba abinci
Sun fito da ransu bayan sun shafe kwanaki 9 a kogon dutse ba abinci

An gano wadansu yara 'yan wasan kwallon kafa su 12 da kocinsu, bayan sun shafe kwanaki 9 a cikin wani katon kogon dutse wanda yake dauke da ruwa a kasar Thailand.

Wadansu mutane masu aikin ceto 'yan kasar Birtaniya sune suka gano inda yaran suke, bayan sun shafe fiye da sati daya suna neman su a wani wuri da yake kusa da birnin Chiang Rai dake arewacin kasar ta Thailand.

DUBA WANNAN: Ruwa ya tafi da mutane 8 a jihar Niger

Iyayen yaran sun nuna farin cikin su matuka, bayan sun ji labarin cewar an gano yaran nasu. Sai dai kuma har yanzu ba a kai ga an fito dasu daga cikin kogon dutsen ba, wanda zurfin shi ya kai kimanin mita 400.

Gwamnan yankin yace zasu cigaba da zuke ruwan kogon, sannan ya aiko da likitoci domin su duba lafiyar yaran.

Yaran wadanda shekarunsu suka kama daga 11 zuwa shekaru 16 sunje wurin kogon dutsen ne a ranar 23 ga watan Yunin nan daya gabata domin yawon bude ido.

A yanzu haka dai masu aikin ceto su din suna ta kokarin kai musu abinci domin su samu karfi a jikin su kafin a cigaba da yunkurin ceto su.

Ma'aikata fiye da 1000 ne suke aikin ceto yaran wadanda suka fito daga kasashen China, Myanmar, Laos, Australia, Amurka da kuma kasar Birtaniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng