Mai ba Shugaba Buhari shawara tayi kaca-kaca da kungiyar CAN

Mai ba Shugaba Buhari shawara tayi kaca-kaca da kungiyar CAN

Wata daga cikin masu ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin yada labarai na zamani watau Lauretta Onochie ta dura kan Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN inda tace su ke hura wutan rikicin Yankin Benuwe da Filato da sauran su a kasar.

Mai ba Shugaba Buhari shawara tayi kaca-kaca da kungiyar CAN
Lauretta Onochie tare da Shugaba Buhari kwanakin baya

Lauretta Onochie tayi amfani da shafin ta na Facebook tayi watsa-watsa da Kungiyar ta CAN. Onochie tace Kungiyar CAN ta Najeriya sun saki layin Ubangiji kuma babu abin da Shugabannin Kiristocin su ke yi sai yaudarar Mabiyan su da nufin tada rikicin addini a cikin kasar.

Misis Onochie wanda ta ke aiki da Shugaban kasar dai tayi dogon rubutu tana sukar Kungiyar CAN inda tace rubutun na ta bai taba sauran Kirsitoci Bayin Allah da ke kaunar Jama’a ba. Onochie tace a lokacin tsohon Shugaban kasa Jonathan, CAN ce ta zama wanda ake ba kudin sata.

KU KARANTA: Makiyaya sun ce Jami'an tsaro na bakin kokarin su

Hadimar Shugaban kasar ta kuma yi tir da yadda Kiristocin Kasar su kayi shiru bayan da ‘Yan Sanda su ka damke wadanda su kashe wan Fasto a Benuwe. Wadanda aka kama din dai duk Kiristoci ne wanda daga ciki akwai David Akenawe, Agada Tsesaa, Tarza Orvanya da Ngyohov Shin.

A rubutun da tayi dai Onochie tace ita rikakkar Kirista ce wanda ta ke aiki da littafin addinin na Kirista mai tsarki don haka ba ta aikata abin da Ubangiji ya hana. Lauretta Onochie ta koka da yadda Kungiyar CAN tayi shiru lokacin da Nnmadi Kanu da Jama’ar sa ke ta tada rikici a Najeriya.

Jiya kun ji labari cewa tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wani abu game da kashe-kashen da ake yi a kasar nan. Gowon yayi kira Gwamnati ta gano masu hannu cikin rikicin inda ya kuma ce addu’a ce za ta ceci kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng