Kamfanin NNPC ta bada tallafin naira N50m ga mutanen da ibtila'in ruwa da iska ya shafa a jihar Bauchi

Kamfanin NNPC ta bada tallafin naira N50m ga mutanen da ibtila'in ruwa da iska ya shafa a jihar Bauchi

Wata babban tawaga karkashin jagorancin Shugaban kamfanin man fetur na kasa,wato NNPC, Engr Dr Maikanti Kachalla Baru, ta ziyarci jihar Bauchi.

Tawagar sun bayar da tallafin kudi har naira miliyan 50 ga mutanen da wannan ibtila'in ruwan sama da iska mai karfi a jihar bauchi ya shafa

Da yake jajantawa Mai martaba Sarkin Bauchi a fadan sa Maikanti ya ce a matsayin sa na dan jihar Bauchi ya kadu matuka da yanda Al'umma ta ta shiga wannan ibtila'in, wanda jama'a da dama suka rasa muhallin su, rayuka da kuma dukiya.

Kamfanin NNPC ta bada tallafin naira N50m ga mutanen da ibtila'in ruwa da iska ya shafa a jihar Bauchi
Kamfanin NNPC ta bada tallafin naira N50m ga mutanen da ibtila'in ruwa da iska ya shafa a jihar Bauchi

Yace wannan jarrabawar babba ce dole ne a gare su su tallafawa jama'a dan babu wanda ya wuci Allah ya jarrabe shi irin haka a rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Kotun musamman da aka kafa sun warware shari’a 324 a Najeriya

Mai martaba Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Sulaiman Adamu CFR, ya jinjinawa tallafin sannan yace za'a isar bisa Amana ta hanyar kwamitocin da aka kafa kan lamarin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa A ranar Juma’a, 29 ga watan Yuni, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta tallafawa wadanda annobar guguwar iska ya ritsa da su a jihar Katsina.

Shugaban kasar yayi alkawarin ne bayan Gwamna Aminu Bello Masari ya lissafa asarar da jihar tayi sakamakon lamarin a matsayin naira biliyan 2.3.

Ya c e ya kasance a jihar domin yiwa wadanda abun ya shafa jaje saboda rashin da aka lissafa ya zarce tunani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng